✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria

Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani…

Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali.

Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris.

A ranar 1 ga Afrilu, Algeria ta sanar cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki mai dauke da makamai a sararin samaniyarta, amma ba ta yi karin bayanin ba.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta ce hukumomi sun tabbatar da “cikakken yakini” cewa an harbo jirgin ne a cikin “A matsayin harin makiya da aka shirya daga gwamnatin Algeria.”

Sanarwar ta ce an gano burbushin jirgin kilomita 9.5 kudu da iyakar Algeria kuma an harbo shi ne da “makami mai linzami.”

Da take bayyana shi a matsayin “abin da bai taba faruwa ba na cin zarafi,” sanarwar ta ce Mali “ta yi Allah wadai da kakkausan harshe game da wannan aikin makiya, rashin abokantaka, da kuma nuna girman kai daga hukumomin Algeria.”

Algeria ba ta yi wani tsokaci nan take game da janye jakadun ba, amma ta sanar a ranar Litinin cewa ta rufe sararin samaniyarta ga jiragen sama da ke zuwa ko tafiya Mali.

Ma’aikatar tsaron Algeria ta ce, “Saboda yawan keta hurumin sararin samaniyarmu da Mali ke yi, gwamnatin Algeria ta yanke shawarar rufe zirga-zirgar jiragen sama da ke zuwa ko tafiya Mali, tun daga yau.”