✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dilolin ƙwaya ke cin karensu ba babbaka a Abuja

Wasu lokutan ma wuraren da ake dillancin kwayoyin nan suna makwabtaka da wasu manyan ofisoshi na tsaron kasa. Wani abin ban mamaki shi ne za…

Rayuwa ta yi wa Talatu atishawar tsaki (ba sunanta na asali ba ne) tun daga shekarar 2018, bayan ta fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin da ƙawarta ta ƙwaɗaita mata yadda lamarin yake.

Ta kasance yarinya mai hazaka mai kimanin shekara 29, kuma ta yi karatu a Jami’ar Kwatano har ta yi aiki a banki na tsawon shekaru biyu kafin ta yi aiki da Kamfanin NNPC da wasu manyan wurare.

Sai dai harkar shaye-shaye ta sa ta siyar da motocinta guda biya da kwamfiyuta da wasu abubuwa masu mahimmanci.

Halin da wakilin Aminiya ya tsince ta a ciki ke nan a Lungun Gurguwa da ke Lagas Street, Garki Abuja. Ta shaida masa cewa, sam ba ta jin dadin wanna rayuwar da take kuma ta yi yunkurin dakatarwa, amma ta kasa, har ahalinta sun shigo cikin lamarin, amma abin ya ci-tura.

Ta ce, “wani lokacin nakan jin kamar zan yi tsirara, idan ban sha kwayoyin da nake sha ba. Ina shan ‘Crack da Tramol”.

To amma fa ba ita kadai ce k cikin wannan halin ba, domin labarinta ya yi daidai da matasa da dama da wakilinmu ya ci karo da su a halin maye a Lungun Gurguwa.

Ku biyo mu cikin wannan binciken diddigi da Wakilin Aminiya ya yi ɓadda-kama, ya shiga wasu manyan wuraren dillancin miyagun kwayoyi da ke da hatsari, domin ganin yadda ake kai hadahadar miyagun kwayoyi masu hatsari a Birnin Tarayya Abuja, duk da hukumomi na cewa suna sanya ido matuka.

Wani bincike da Majalisar dinkin Duniya ta gudanar karkashin ofishinta da ke yaki da miyagun kwayoyi (UNODC), tare da Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) a shekarar 2018 ya ce, kimanin kashi 14.4 na ‘yan Nijeriya ne ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi, wanda hakan ya fi kaso 5.6 na fadin duniya.

Abuja gari ne da ke da sarkakiya da kuma yankuna daban-daban, bugu da kari ga matakan tsaro, amma a haka ake dillancin miyagun kwayoyi ido na ganin ido a cikin kwaryar birnin. Wasu lokutan ma wuraren da ake dillancin kwayoyin nan suna makwabtaka da wasu manyan ofisoshi na tsaron kasa. Wani abin ban mamaki shi ne za a iya yi wa mutum safarar miyagun kwayoyi har inda yake a Abuja.

Kafin mu fara wannan bincike sai da muka yi kuturunka nawa a gari domin gano inda ake wannan dillanci fiye da kowane yanki. Yawancin mutanen da suka ba mu amsa sun shaida cewa, shiyyar ‘Area 1’ da ke yankin Gundumar Garki a Abuja ta zama wata matattarar dillalan miyagun kwayoyi, inda kowace irin ƙwaya kake nema za ka samu a nan.

Wani wuri da shi ma aka ambata shi ne wani tsauni da ake kira da Tora-Bora duka a yankin Area 1 din.

Wasu wuraren da hukumomi suka ce suna sanya ido sun hada da Mabushi da Gwagwalada da Dei-Dei da Wuse da ma Gwarimpa.

Abbubuwan da ke faruwa a ToraBora

A binciken da muka gudanar, mun gano cewa, Tora-Bora bai wuce mita 100 daga inda ofishin rusasshiyar rundunar ‘yan sanda ta SARS yake ba, kuma bugu da kari ‘yan mitoci kadan ana iya ganin ofishin Hukumar Leƙen asiri ta Ƙasa (NIA).

Wakilinmu ya samu damar hawa saman wannan tsauni tare da taimakon wani da ya amince ya yi masa rakiya har cikin wurin. Tsaunin yana kan babban titin Murtala Muhammad da ke Gundumar Garki.

Wakilinmu na isa saman wannan tsauni, inda suka ci karo da wasu matasa uku, wadanda da alama su ne masu gadi da leken asiri.

Waɗannan matasan ba za su bar kowa ya wuce ba, idan ba a san shi ba watakila kada ya kasance jami’in tsaro ne aka ingizo musu shi, inda suka fara yi wa wakilinmu tambayoyi, amma aka ci sa’a wanda ya yi masa rakiya ya san wani dila a wajen, wanda suna tsaye sai ga shi ya bullo kuma suka cafke hannu.

Ana kiran dilan da suna Babban Yaro, kuma shi ma matashi ne da bai wuce shekara 25 ba, shi ne ya yi masa jagora zuwa ciki. Tora-Bora matattarar dillalan miyagun kwayoyi ce da wakilinmu ya hangi matasa da mata wasu na shaye-shaye wasu kuma na kasuwancinsu

Daga nan Babban Yaro ya kira wani daga cikin yaransa, ya kawo mana kwalbar Kodin, wanda maganin tari ne na Barcadin, amma yana bugarwa, inda masu shansa suke cewa, yana ba su caji, amma tuni Gwamnatin Nijeriya ta haramta sarrafa shi da siyar da shi a shekarar 2018.

Wakilin da ya yi ɓaddakama ya samu damar siyan wasu miyagun kwayoyi irin su Kolos da Loud, wadanda samfurin tabar Wiwi ne da kuma kwayar Tramol ko a ce Rafanol. A Tora-Bora kana iya samun duk kalar miyagun kwayoyin da kake so idan ka san dilan da ya dace.

Ba a Tora-Bora ƙadai ba ne

A Lungun Gurguwa da muka fara kawo dazu, abin da ke faruwa a wannan layi yana da daukar hankali.

Da isar wakilin Aminiya wannan wuri matasa ne ya hango birjik sun yin mankas, sun sha kwayoyi. Ya ci karo da wani matashi ya sha Kolos har ya yi amai a wajen, inda ta kai har ba ya iya tsayawa da kafarsa ga yawu na malala a bakinsa.

A layin Lungun Gurguwa da ke Legas Street a Garki, yawancin abubuwan da ake siyarwa su ne Kolos da Loud da CK, wanda wani samfurin Koken ne mai karfi. Barau da ya yi min jagora ya ce matasa da dama a wanna layin ba su da aiki sai wannan shaye-shaye. “Amma kuma suna da manyan iyayen gida da suke kawo musu kwayoyin” in ji shi.

Abin mamaki a kusa da inda gungun matasan ke taruwa, suna shan miyagun kwayoyi da dillancinsu, akwai ofishin ‘yan sanda na Garki.

Wakilinmu da ya je a matsayin dan kallo kawai, inda ya lura hadahada da kwararowar mashaya kwayar ya karu daga misalin karfe 9 zuwa 11 na dare.

Alex ya ce: “CK na iya bugar da mutum ya kasa motsin. Haka ma Kolos, ita ma wata kalar tabar Wiwi ce mai karfin gaske. Wadanda ba su iya siyan ainihin koken, suna dafa ta hoda ibilis.”

Me ya sa ‘Area 1’ ya yi ƙaurin suna?

Eriya Wan (Area 1) da kowa ke yawan magana a kai wani yanki ne na Abuja da ke Gundumar Garki da ake gudanar da kasuwanci daban-daban. Sai dai inda ake maganar dillancin miyagun kwayoyi yana tsakiyar unguwar ce.

Wakilinmu tare da dan jagorarsa Barau (Ba sunansa ba ke nan), wanda shi ma tsohon dilan kwayoyi ne, amma ya tuba a yanzu, yana da kyakkyawar alaka da dilolin har yanzu, kuma suna isa wajen wakilinmu ya lura yadda ake hadahadar kasuwanci, ba kowa zai yi tunanin a nan ake badakalar ba.

Shi dai wannan wuri da ake magana yana boye ne a bayan tashar motoci da ake kira da ‘Gwagwalada Park’ a Area 1. Shaguna ne ke kewaye da wurin daga masu soya kosai da masu siyar da abinci da faci da sauransu.

Barau ya c,e “Ko kana da kudi ba za ka iya shiga wurin ba, idan ba ka san wani ba, domin babu wanda zai ba ka hadin kai. Manyan mutane suna zuwa wajen, suna siyan kwayoyi, kamar kamfani ne a nan. kananan diloli a nan suke zuwa su siya, domin su je su siyarwa masu sha. Wannan wuri ne mai hatsari”.

Wakilinmu ya yi ɓadda-kama a matsayin wanda yake son shiga kasuwancin safarar miyagun kwayoyi, domin ya gano ya ake harkar, kuma aka ci sa’a aka haɗa shi da wani dila da ake kira da ‘Kawu’.

Da alama kuma yana da karfin fada a ji a wajen, domin da wakilinmu ya bukaci samfurin CK nan take ya kira yaronsa, ya kawo giram daya a kan Naira 25,000 daga bisani kuma ya nuna masa yadda ake siyarwa.

Ya yi masa alkawarin in har aka ji dadin kasuwanci to zai hada shi da manyan “ƙwari” wadanda za su tsaya masa a komai, sannan kuma da yadda zai iya safara hankali kwance. Ya ce, yawanci ana kawo musu CK ne daga Legas kuma duk giram daya ana kawo ta a kan naira 6,000.

Kawu ya shaida masa cewa, “idan kana so ka tafi da kwayoyi ba wanda ya gane, to kawai ka doye su cikin matse-matsinka. Jami’ai ba za su matsa maka wajen bincike.”

A wurin da ake dillancin miyagun kwayoyi wasu kananan shagunan kiyos ne suke amfani da su a matsayin dakunan kwana da kuma maboyarsu da ajiye kwayoyin.

Matasa ne birjik a wannan wuri suna ta shayeshaye ba tare da wata damuwa ba, domin a cewar Barau manyan ‘ya’yan masu kudi da wasu jami’ai ma suna zuwa wajen domin siya ko karbar “kasonsu”

Wani wuri da kananan dilolin kwaya ke cin karensu ba babbaka shi ne ‘Wuse 2’ inda nan ma da wakilinmu ya ziyarta ya ga yadda ake masa lale marhabin da neman siyar masa duk kwayar da yake bukata, duk da yake jami’an tsaro na gilmawa jefi-jefi, amma bai hana su ci gaba da harkokinsu ba.

Yadda ake safar miyagun ƙwayoyi a Abuja da kewaye

A zantawar da wakilin Aminiya ya yi da Ibrahim Yusuf Gashinbaki, mataimakin Shugaban kungiyar ’Yan Banga ta kasa da ke kula da Birnin Tarayya Abuja ya ce, suna iya bakin kokarinsu na ganin sun taimaka wa jami’an tsaro wajen dakile yaduwar miyagun kwayoyi.

“Idan mun kama, mukan mika wa ‘yan sanda su yi bincike ko kuma Hukumar NDLEA, amma abin da zai ba ka mamaki shi ne yadda suke fitowa kwanaki kadan bayan kama su”, in ji shi.

Ya bayyana cewa, yawancin masu motocin haya suna taka rawa wajen safarar miyagun kwayoyi, domin ana amfani da su wajen cim ma hakan. Wasu rukunin mutanen da ya yi zargi su ne masu tuka mashinan “Power Bike”, inda ya ce suna yawan safarar miyagun kwayoyi kuma an sha kama su da hakan.

“Mun sha kama su sosai a kan mashinansu, daga wajen mutumin da ba ka yi tunani ba ma”

Ya kuma yi zargin cewa, wadannan mutane suna da wasu manyan masu fada a ji da suke tsaya musu a lamuransu.

Wakilin Aminiya ya zanta da wani tsohon dilan miyagun kwayoyi a Abuja, wanda shi ma ya ce ya tuba a yanzu, inda ya ce a lokacin da yake hadahadar kwayoyin, babu yadda bai sha kamu ba, amma yakki bari har zuwa 2018.

Ya ce, a lokacin yadda suke samun miyagun kwayoyi hanya ce mai sauki: “Yawancin jami’an da ke kamawa su ne suke zuwa, su siyar wa dillalan bayan sun kwace daga hannunmu. Sai su je su sake siyar wa wasu. Babu wanda ba ya siyarwa, ai duk wadanda ke kamawa suna siyarwa”, in ji shi.

Wani dilan shi ma ya shaida wa wakilinmu cewa, masu zirga-zirga da motoci daga Abuja zuwa wasu jihohi na taka rawa wajen safarar miyagun kwayoyi, “domin da su ake haɗa baki, saboda jami’ai ba su cika bincika direba ba.”

Sai dai a tashar Area 1 da wakilinmu ya ziyarta, domin ganin ko za su amsa wani sako da ya naɗe a cikin leda mai kama da kwayoyi, direbobin sun ki amsa inda suka bayyana fargabarsu da nanata yadda jami’ai ke matsa musu a ’yan kwanakin nan. Dilan ya ce, “ai ba za su amsa ba, dole sai wanda suka aminta da shi, saboda kada a saka musu tarko.”

Aminiya ta gabatar da wadannan zarge-zarge ga Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA, amma kakakin hukumar, Femi Babafemi ya karyata su, inda ya ce babu wanda zai iya yin kafar ungulu ga dokokinsu, domin akwai ka’idoji masu tsauri a kan miyagun ƙwayoyi a hukumar.

“Babu wanda ke da hurumin shiga dakin ajiye magungunan da muke kamawa shi kadai ba tare da sahalewar akalla mutum uku ba”, in ji Babafemi

Ya ce, tuni suka dade da gano irin wadannan wuraren da Aminiya ta gano kuma suna iya bakin kokarinsu na fatattakar su ba kakkautawa.

Mun kama dilolin ƙwaya 1,819 a Abuja cikin shekaru — NDLEA

Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kan Kama’a na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa, tsakanin 2022 zuwa 2025, hukumar ta kama mutum 1,819 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Abuja. 1,738 daga cikin maza ne sai mata 81. A cikin shekaru ukun kuma hukumar ta kama miyagun kwayoyi da suka kai kilo 33,510.3 da lita 293.1 na kodin.

Babafemi ya ce, duk da kokarin da ake yi, amma dillalan miyagun kwayoyi suna sauya salo a kowane lokaci, inda suke canza matsugunai da zarar an fatattake su a wani wurin.

Aminiya ta tuntubi Rundunar ‘Yan sanda, reshen Birnin Tarayya Abuja, a kan ko me za ta ce game da ganin cibiyoyin ‘yan sanda a kusa da inda ake harkar dillancin miyagun kwayoyi.

SP Josephine Adex, ita ce kakakin rundunar ta ce, suna aiki kafada da kafada da Hhukumar NDLEA, domin ganin sun fatattake su, kuma yanzu haka sun gano wasu wurare masu mahimmanci da za su kaddamar musu.

“Babu yadda za a yi hukumar ‘yan sanda ta kau da kai game da irin wannan abu da yake faruwa, kuma kwanan nan za a ga sakamako mai kyau.”

Me dokar ƙasa ta ce?

Sashi na 11 (d) na Hukumar NDLEA ya haramta sha da fataucin miyagun kwayoyi, kuma duk wanda aka kama da laifin zai fuskanci tara da kuma zaman gidan kaso. Dokar ta ce, za a iya daukar mataki mai tsauri kan wanda aka kama yana da hannu a ciki.

Za a iya yanke wa duk wanda aka samu da laifi hukuncin dauri a gidan kaso daga shekara 15 zuwa 25. A wasu sassan dokar ma an ce, za a iya yanke wa mai laifin hukuncin daurin rai da rai idan abin ya yi yawa.

Kodayake Majalisar kasa ta yi nazarin sashin kisan kai ko daurin rai da rai a shekarar 2024, inda ta maye gurbinsa da yanke hukunci mai tsauri kan wanda aka samu da laifin kuma a kwace abin da aka kama.

Dokar da aka amince da ita yanzu haka tana gaban Shugaban kasa Tinubu domin rattaba mata hannu.

 

Wannan rahoton ya samu tallafin Gidauniyar Daily Trust (DTF) haɗin gwiwa Gidauniyar MacArthur.