✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani abu ya fashe kusa da barikin soji a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ya tayar da bam ɗin ya mutu.

Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Josephine Adeh, ta ce tuni ta tura jami’anta wajen domin bincike da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“A ranar 26 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 2:15 na rana aka yi mana kiran gaggawa kan wani abu ya fashe a shatale-shatalen hanyar Mararaba-Nyanya.

“Muna samun rahoton jami’anmu da ke sashen da abun ya shafa suka dira a wajen in da suka kange wurin.

“Mun samu nasarar ceto mutum guda da ya samu rauni, kuma yana asibiti yana karɓar magani.

“Muna nan muna bincike domin gano abin da ya fashe, da kuma musabbabin hakan.

Daga nan ne rundunar ta bukaci al’ummar yankin su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, su kuma miƙa wa rundunar duk wani motsi da ba su amince da shi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ya tayar da bam ɗin ya mutu.