Wata rana wani kwarto ne ya bi tsohuwar budurwarsa gidan mijinta, sai ya yi kicibus da maigidanta, nana fa a ka fara zaro zance ana habaici duk a tunaninsu mijin ba zai fahimta.
Kwarton da tsohuwar budurwarsa sun rika yi wa juna baa da jefa batun bukatarsu a fakaice.
Ga yadda suka kasance a tsakaninsu:
Kwarto: Assalamu alaikum.
Miji: Amin wa’alaikumussalam, sannu da zuwa, zauna mana.
Kwarto: To amma me ya sa matarka take hararata?”
Matar: Harararka kamar yaya? Gafara can da fuskarka kamar je-kadawo-an jima.
Kwarto: Ji min mata! Gafara can da kafarki kamar ba zan dawo ba, sai dai ki same ni a gida.
Miji: Ke tawa, me ya sa kike cin zarafinsa haka?
Matar: Dole in ci zarafinsa, da hancinsa kamar zan zo gobe da safe karfe bakwai.
Kwarto: Ni ba zan kara yi miki magana ba, da bakinki kamar kada ki makara.
Miji: Malam gara mu je waje mu yi hira, mu bar mata gidan da wannan fadan naku kamar gobe za ku ci ubanku!
Daga Mustapha Bashir Yahuza Malumfashi, 07065635644