Wata matar aure Deborah Joseph ta nemi kotu da ke zamanta a Mararaba, Jihar Nasarawa ta raba aurenta da mijinta bisa zargin yana kokarin yin tsafin kudi da dansu.
Deborah ta shaida wa kotun cewar mijin nata ba ya kulawa da bukatunsu na rayuwa, sai dai kullum ya zo gida da tsakar dare mankas cikin giya.
Ta kuma ce mijin nata bai biya ta sadaki ba, “Ina kuma da kananan yara amma kulum ni ke ciyar da su, na kuma biya kudin baya”, inji matar.
Da yake kare kansa, mijin nata ya karyata zargin da cewar bai taba rashin kulawa da iyalinsa ba tun da suka yi aure. Kuma bai taba bugun ta ba.
“Matsaloli sun fara shiga tsakannmu ne tun lokacin da na rasa aikina. Ina rokon kotu da kar ta amince da bukatarta ta raba aurenmu”, inji shi.
A hukumcin da ya yanke, Mai Shari’a Ibrahim Shekarau ya nemi ma’auratan da su koma gida su sassanta kansu.
Ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa 12 ga watan Agusta domin yanke hukumci.