✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mauludin Kaduna: MDD ta nemi Najeriya ta biya diyyar mutanen da jirgin soji ya kashe

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Najeriya ta biya diyya tare da kulawa da duk mutanen da jiragen soji suka kai wa hari a kasar

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya diyya ga duk mutanen da jiragen soji suka kai wa hari a kasar.

MDD ta kuma yi tir da harin bom da sojojin Najeriya suka kai da jirgi mara matuki kan taron Mauludi a yankin Tudun Biri a Jihar Kaduna bisa kuskure.

Majalisar ta kara da cewa harin na daren Lahadi da aka kashe fararen hula akalla 85 ba shi ne farau ba, don haka dole gwamnati da sojojin kasar su dauki matakin hana sake faruwar hakan.

“Muna kira ga gwamnatin Najeriya ta yi zuzzurfan bincike kan karya dokar kasashen duniya da aka yi wajen kashe fararen hula tare da kuma raunata da a harin jirgin sojin.

“Sannan gwamnati ta ba da diyya da cikakkiyar kulawa ga duk mutanen da jiragen soji suka kai wa irin wadannan hare-hare.

“Dole ne kuma rundunar tsaron Najeriya ta yi nazari tare da inganta dokoki da tsarin aikinsu domin kauce wa irin haka,” a cewar kakakin MDD, Seif Magango a ranar Larba.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta dauki alhakin harin, wanda ta ce jirgin ta ya yi kuskuren jefa bom kan fararen hula a lokacin da take fatattakar ’yan ta’adda a yankin karamar Hukumar Igabi.

Rundunar sojin ta bayyana cewa ibtila’in ya faru ne bayan da ta yi kuskuren fassara motsin fararen hular da ke halartar taron Mauludin a matsayin ’yan ta’adda, har ta jefa musu bama-bamai.

Amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce, “Mun kadu da abin da sojojin suka fada cewa sun yi kuskuren fassara motsin fararen hular … wani babban abin damuwa shi ne harin ya saba wa dokokin kasashen duniya.”

Igabi na cikin yankunan jihar Kaduna da suka ’yan ta’adda da fi addaba, inda suke yin kisan gilla suna kona dukiyoyi ko sacewa, tare da garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.