’Yan sanda sun cafke matar da suke nema bisa zargin ta da burma wuka a cikin wata ’yar makwabtakanta mai shekara takwas a Jihar Kano.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ya ce matar ta shaida wa masu bincike cewa ta yi haka ne domin hallaka yarinyar saboda tana zargin mahaifin yarinyar na zuga mijinta ya kara aure.
Da take amsa tambayoyin ‘yan jarida a ranar Juma’a a hedikwatar runduar, wacce ake zargi ta bayyana cewar ta sayi wuka ta N300 a unguwar da ta aikata laifin, kuma ta caka mata.
“Na yi hakan ne don nakashe ta. Amma ba ta mutuba. Ina rokon a yi min afuwa. Wallahi na yi zargin mijinta yana bawa mijina shawara a kan ya karo aure. Idan ya karo aure za mu shiga wani hali,” in ji ta.
- ‘Tsarin shiyya-shiyya barazana ce ga cin gashin-kan Majalisa’
- An kama tirela makare da naman jaki na N23m a Kebbi
Ta yi bayanin ne a lokacin da aka gabatar da ita bayan ranar Alhamis an kamo ta daga inda ta je ta boye a kauyen Dungulmi da ke Karamar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.
Aminiya ta ruwito cewa matar ta yi layar zana bayan da ta yi wa yarinyar wannan danyen aiki a unguwar Kureken Sani, bayan da ta dauko yarinyar daga wurin iyayenta a unguwar Gadon Kaya a matsayin ’yar rakiya.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, wani bawan Allah ne ya sanar da rundunar bayan an tsinci yarinyar da wukar da aka luma mata daga bangaren cikinta na dama, ya fito ta bangaren hagu, a cikin wani kango
Ya ce mutumin ya shaida musu cewa wukar ta makale a cikin yarinyar, sannan an ji mata raunuka a jiki, inda aka garzaya da ita zuwa asibiti domin ceto rayuwarta.
“Bayan farfadowar yarinyar mai shekaru takwas ta bayyana cewa wata makwabciyarsu ce ta kai ta kangon ta caka mata wukar, sannan ta tsere.
“A yayin binciken farko an tsare mijin matar, wanda ya ce tana da tabin hankali kuma bai san inda ta shige ba.
“Amma bayan zurfafa bincike an kamo matar mai suna Fatima a inda ta boye a kauyen Dungulmi da ke Karamar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa,” kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kanta.
Ya ci gaba da cewa binciken zai kuma gano gaskiyar batun tabin hankalin da mijinta ya ce tana fama da shi, domin akwai alamar tambaya a kan maganar.