Kotu ta tisa ƙeyar wata matar aure zuwa gidan yari kan zargin soka wa mijinta wuƙa har lahira.
Mai Shari’a Misis Olabisi Ogunkanmi ce ta ca da umarnin tsare matar mai shekara 33 a duniya.
Babbar Kotun Majiatare da ke zamanta a Ibadan, a Jihar Ondo, ta bayar da umarnin ne bayan ta yi watsi da ikirarin wadda ake zargin cewa kotun ba ta da hurumin saurar shari’ar.
Daga nan kuma ta daga zaman zuwa ranar 25bga watan Maris, 2025.
An gurfanar da wadda ake zargin ne kan laifin aikata kisa, idan ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Kofur Akeem Akinloye, cewa a ranar 30, ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 9 na dare da daɓa wa mijinta mai shekara 39 wuƙa, ya ce ga garinku nan.
Jami’in ya shaida wa kotu cewa matar ta halaka mijin nata ne a yayin da suka samu saɓani tsakaninsu a gidansu da ke garin Ibadan.
Hakan a cewarsa laifi ne ƙarƙashin sashe na 316 da 319 na dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Oyo.
(NAN)