Gamayyar Malaman Addinin Musulunci mata a Jihar Kano sun gudanar da addu’o’i don neman wanzuwar zaman lafiya da tsadar rayuwa a jihar da kuma kasa gaba daya.
Matan sun gudanar da addu’o’in ne a karkashin jagorancin Malama Fatima Nabulusi Bako da Malama Fatima Muhammad Fagge.
A yayin gudanar da addu’o’in matan sun yi saukar Alkurani sau 19.
A jawabinta tun da farko, Shugabar tagwayen tashoshin gidan rediyo da talabijin na Rahma da ke Jihar Hajiya Binta Sarki Mukhtar wacce kuma daya ce daga cikin masu shirya taron, ta bayyana cewa sun shirya shi ne don neman mafita wurin Allah game da halin da aka samu kai a ciki na tsadar rayuwa da kuma zaman dardar da ake ciki na yiwuwar barkewar yaki a tsakanin kasashen Najeriya da kuma Nijar.
Ita ma a jawabinta Hajiya Iya Lukat ta bayyana cewa akwai buqatar mata su kara yin hakuri wajen tattala abin da mazajensu suka kawo cikin gida tare da tallafa wa mazajen nasu wajen kula da iyalinsu..
Shugabar mata Musulmi ta Kasa reshen Jihar Kano (FOMWAN) Malama Khadija Muhammad ta ce a wannan lokaci babban abin da iyaye za su yi shi ne mayar da hankali wajen yi wa ’ya’yansu tarbiyya ta gari.
“Muna kira ga iyaye da su zage dantse wajen tarbiyyar ’ya’yansu duba da irin halin da ake ciki na tabarbarewar tarbiyya.
A jawabansu daban-daban malaman da suka jagoranci adduar sun nemi malaman sun kuma yi kira ga shugabanni a kowane mataki da su taimaka wa al’ummarsu duba da halin kunci da alumma suka shiga.
“Babu shakka jamaa’ na cikin wani hali na matsi. Aure da yawa yana tangal-tangal saboda magidanta ba sa iya sauke nauyin iyalinsu. Yara da yawa ba su fahimtar karatu saboda halin yunwa da suke ciki. Don haka muke kira ga mahukunta da su ji tsoron Allah su duba halin da ake ciki. Su tuna fa talakawan nan ne suka fito suka zabe su har suka kai ga kujerar da suke kai.”
Matan wadanda suka taru a inuwa guda ba tare da bambancin akida ba sun nemi daukin Allah dangane da halin da mazajensu suka shiga na rashin wadatar abinci a gidajensu.