✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai Kula da Kabarin Manzon Allah ya rasu

Marigayi Sheikh Abdul Aziz bin Al Falah ya kasance mai kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake.

Allah Ya yi wa Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah, Mataimakin Shugaban Majalisar Masallacin Madina da ke kasar Saudiyya, rasuwa.

Kafin kafin Allah Ya dauki rayuwarsa, marigayi Sheikh Abdul Aziz bin Al Falah ya kasance mai kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake.

Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah ya koma ga mahaliccinsa ne a ranar Talata, kamar yadda hukumar gudanarwar masallacin ta sanar.

“Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah, wanda ya jima yaba rike da mukamin Mataimakin Shugaban Masallacin Annabi da ke birnin Madina ya rasu ne ranar Talata.

“Muna rokon Allah Madaukaki ubangji ya gafarta masa kuma ya jikan sa,” in ji sanarwar masallacin.