✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mata ta nemi kotu ta nema wa ɗanta uba daga cikin mazajenta biyu

Matar dai ta ce ta kasa gane hakikanin mahaifin dan nata a cikinsu

Wata mata mai suna Shamsiyya Yunusa ta nemi Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey a Jihar Kano da ta nema wa danta mahaifinsa daga cikin maza biyun da ta rabu da su.

Shamsiyya, wacce ke zaune a unguwar Darmanawa a birnin na Kano dai ta shaida wa kotun cewa ta haifi danta kimanin wata hudu da komawarta gidan mijinta na farko Safiyanu Hashim bayan aurenta ya mutu da mijinta na biyu Rabi’u Sani.

A cewarta, ta shafe tsawon shekara guda a gidan iyayenta bayan mutuwar aurenta da mijinta na biyu, inda daga bisani kuma ta yi kome gidan mijinta na farko.

Ta bayyana wa kotun cewa bayan ta rabu da mijinta na farko, ta yi batan-wata na tsawon watanni biyar inda ta yi zaton alamu ne na juna biyu. Daga baya kuma sai jini ya zo mata inda ta yi zaton bari ta yi. Bayan jini ya ci gaba da zuwa mata sai ta sake yin aure.

Sai dai mijin nata na farko Safiyanu ya bayyana cewa sun zauna zaman aure tsawon shekara shida inda bayan sun rabu ta auri Rabiu, bayan sun rabu da mijinta nata na biyu sai ya sake auren ta a watan Janairu 2022 inda kuma ta haihu a watan Afrilu 2022, wata 3 da kwana 11 bayan aurensu.

A nasa bangaren, Rabiu ya shaida wa kotun cewa sun zauna zaman aure na tsawon watanni biyu kafin annobar Kwarona.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Abdullahi Halliru Abubakar, ya umarci Safiyanu da ya kawo wa kotun katin gayyatar aurensu na farko ko satifiket din aurensu, kafin daga bisani kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Disamban 2023.

%d bloggers like this: