✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 Sun Mutu Wasu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Abiya

Akalla mutum hudu ne suka mutum a lokacin da babbar motar dakon kaya ta yi awon gaba da wata bus da Keke NAPEP.

Akalla mutum hudu ne suka mutum a lokacin da babbar motar dakon kaya ta yi awon gaba da wata bus da Keke NAPEP.

Al’amarin ya faru ne a ranar Talata a kan gadar Ogbor-Hill da ke garin Aba a jihar Abia, lokacin da burkin babbar motar dakon kayan ya shanye.

Rahotanni sun ce bayan faruwar hadarin, mutane sun rika fito da fasinjojin ababen hawan da babbar motar ta take, sai dai baya ga wadanda suka rasu, akwai karin mutane da dama da suka samu munanan raunuka.

Wani ganau ya ce ‘mun rika ciro mutanen ne saboda babu motar janwe da za a yi anfani da ita wajen fito da ababen hawan da ke karkashin babbar motar.’

An hango Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC a wajen da abun ya faru.