✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: BUK Ta Dakatar Da Jarabawa

Wannan na zuwa ne bayan fara yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka shiga a ranar Talata.

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta dakatar da jarabawar zangon farko shekarar 2022/2023 sakamakon yajin aikin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara.

Sanarwar da mai rikon mukamin magatakardan jami’ar, Amina Abdullahi Umar, ta fitar ta bayyana cewa hakan ya zama dole ne bayan yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka tsunduma.

Ta bukaci daliban jami’ar da su kwantar da hankalinsu tare da jiran umarni na gaba, kuma “da zarar an kammala yajin aiki za a ci gaba da zana da jarabawar.”

A ranar Litinin ne kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka fara.

Yajin aikin na zuwa ne a matsayin martani ga cin zarafin da ake ’yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Imo suka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, amma wadanda ake zargin sun musanta.

Tuni dai ayyuka suka samu cikas a fadin Najeriya a sakamakon yajin aikin da aka fara ranar Talaat.