✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu ranar daina amfani da tsofaffin kudi —CBN

CBN ya ce babu raina daina amfani da tsofaffin kudin sabanin wa'adin da aka yanke da fari.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira kuma za su ci gaba da kasancewa halastattu har bayan wa’adin 31 ga watan Disamban 2023 da aka sanya. 

Wata sanarwa da daraktan sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin ya fitar, ta bukaci ’yan Najeriya  CBN bukaci mutane su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira na 200, 500 da kuma 1000 har sai abin da hali ya yi.

Sanawar ta CBN ta kuma umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hadar-hadar kudi da su ci gaba da karbar tsofaffi da sabbin takardun Naira.

Ya bayyana cewa CBN ya ce an dauki matakin ne daidai da tsarin hada-hadar kudi ta kasashen duniya da kuma hana faruwa halin matsi da aka shiga a baya.

Sanarwar ta kara da cewa bankin CBN yana aiki da sauran hukumomi don ganin an janye karar da kuma soke umarnin kotun da sanya wa’adin na ranar 31 ga watan Disamba.

A watan Oktoban 2022 ne tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya jagoranci kaddamar da tsarin sauya fasalin takardar Naira na 200, 500, da kuma 1000, kuma ya ba da wa’adin dakatar da karbar tsoffin takardun kudin.

Matakin na Emefiele ya zo ne gab da babban zaben 2023, wanda da ya jawo zargin gwamnan bankin ya yi hakan ne domin kayar da jam’iyyar APC mai mulki, bayan ya fadi zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta.

Dambarwar sauyin kudin da kuma takaita cirar tsabar kudi a lokacin ya jefa ’yan Najeriya cikin tashin hankali da matsin rayuwa, wanda haka ya sanya wasu gwamnoni maka shi a kotu suna kalubalantar umarnin daina amfani da tsofaffin takardun kudin.