Ƙungiyar ‘yan canji ta Najeriya (ABCON) ta bayyana cewa a yanzu mambobinta na sayen duk dala ɗaya a kan Naira 980 a kasuwar bayan fage sannan suna sayar da ita kan Naira 1,020.
Shugaban Ƙungiyar ABCON, Aminu Gwadabe ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake gabatar da wani shiri kan Kasuwanci a tashar Talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa Naira ta ƙara daraja fiye da yadda ake tsammani idan aka kwatanta da darajarta a watannin baya.
- Taliban ta dakatar tashoshin talabijin biyu saboda cin zarafin Musulunci
- CBN ya sake karya farashin Dala
Gwadabe ya yaba wa gwamnati da Babban Bankin Najeriya bisa ƙoƙarin da suka yi ya zuwa yanzu, inda ya ce wannan ne karo na farko a cikin shekaru 15 da suka gabata da farashin dala a kasuwa ya yi ƙasa.
Ya ƙara da cewa yanzu an samu kwanciyar hankali a kasuwar saboda hasashen wanda ya kasance ɗaya daga cikin abin da ke kawo taɓarɓarewar abubuwa.
Gwadabe ya ce: “muna sayen duk da dala ɗaya a hannun gwamnati kan Naira 980 kuma muna sayar da ita kan Naira 1,020 a halin yanzu.