✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa

Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa shahararren mai sana'ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa.

Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007.

Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya a yayin da yake rawa.

Bayan lauyan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Zarami Mohammed, ya gabatar da hujjojin karar tare da shaidar bidiyo a kotu. da kuma amsar laifin Huseini, Mai Shari’a Shuaibu ya ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

Hukumar EFCC ta ci gaba da gargadin jama’a game da bata ko kuma yin amfani da takardun Naira ba daidai ba, musamman a lokacin bukukuwan jama’a, tana mai bayyana irin wadannan ayyukan a matsayin zagon kasa ga tattalin arziki.