✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati 

Ma'aikatar ta ce matakin ba ka wucin-gadi ba ne.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace a farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka.

Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi.

Ma’aikatar Kuɗi ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce wannan ba mataki ne na wucin-gadi ba, sai dai tsari ne da ake son ya ɗore wanda Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta aminta da shi.

“Wannan manufa za ta taimaka wajen bunƙasa tace mai a gida, rage dogaro da dala, da kuma inganta tsaro a fannin makamashi a Najeriya,” in ji Ma’aikatar.

“Wani muhimmin ɓangare ne na shirin gwamnati don kare makomar tattalin arziƙin ƙasa.”

A ranar Talata ne manyan jami’an Ma’aikatar Kuɗi, NNPCL, FIRS, CBN, da wasu manyan hukumomi suka gana domin duba yadda aikin ke tafiya da kuma magance matsalolin da ka iya tasowa a tsawon lokacin aiwatar da shirin.

“Mun fahimci cewa sauye-sauye irin wannan suna zuwa da ƙalubale,” in ji wani jami’i daga cikin mahalarta taron.

“Amma dukkanin hukumomin da ke da hannu a cikin shirin sun ƙudiri aniyar ganin an cimma nasara.”

A baya-bayan nan NNPCL ya daina sayar wa matatar Dangote ɗanyen mai a farashin Naira bayan ƙarewar yarjejeniyar da suka ƙulla.

Hakan ya haifar da tashin farashin man fetur a gidajen mai a faɗin ƙasar nan, lamarin da masana suka ce hakan zai sake shafar tattalin arziƙin Najeriya.