Tsohon shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, Kwamared Ali Ciroma ya rasu.
Ya rasu ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
- Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai rancen kuɗin karatu
- DAGA LARABA: Yadda Sabbin Ma’aurata Ke Morewa A Ramadan
Sakataren Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Jihar Borno kuma ɗan uwansa, Ali Ibrahim Ciroma ne ya sanar da rasuwar Ali Ciroma a madadin iyalansa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Cike da alhini nake sanar da rasuwar Kwamared Ali Ciroma, tsohon Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya.
“Marigayin ya rasu ne da yammacin yau [Talata] a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
“Marigayi Kwamared Ali Ciroma ya kasance shugaban NLC daga tsakanin 1984 zuwa 1988.
Ya kuma kasance shugaban ma’aikatan lafiya na karkara na Najeriya a shekarar 1960 kafin daga bisani ta zama Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da kasa.