Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba.
Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato ta fara biyan sabon albashin tun a watan Janairu ga dukkanin ma’aikatan jihar, ciki har da na ƙananan hukumomi.
Ya ce: “Sakkwato ce jiha ta farko da ta fara biyan sabon albashi na dubu 70, kuma ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi na amfana da shi.
“Maganar shugaban NULGE na ƙasa ba gaskiya ba ce.”
Ya ƙara da cewa bai kamata shugaban NULGE ya faɗi irin wannan magana ba tare da ya bincika gaskiyar al’amari ba.
Kwamared Aliyu, ya yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu bisa ƙoƙarinsa na biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu da kuma dawo da kuɗin tafiyar da ofisoshi, biyan bashin fansho da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.
Sai dai wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa ba dukkanin ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar ne ke karɓar albashin dubu 70 ba.
Wani ma’aikaci ya ce: “Wasu daga cikinmu da muke karɓar dubu 18 a da, yanzu muna karɓar dubu 30, yayin da waɗanda ke karbar dubu takwas a baya, yanzu gwamnati na biyansu dubu 20.”
Wannan ya nuna cewa duk da gwamnati na ƙoƙarin biyan sabon albashi, har yanzu ba a kai ga kowa ya samu dubu 70 ba a matakin ƙananan hukumomi.