Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga bayan labule da jagororin Majalisar Dattawa a Yammacin wannan Talatar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci tawagar sanatocin da ta kai wa shugaban ƙasar ziyara kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
- Gwamnatin Sakkwato za ta kashe N6.7bn wajen ciyarwar Azumi
- Majalisa ta dakatar da Sanatan da ya ce an yi cushen N3trn a Kasafin Kuɗi
Ganawar dai na zuwa ne sa’o’i bayan da Majalisar Dattawan ta dakatar da Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi har na tsawon watanni uku kan sukar da ya yi dangane da Kasafin Kuɗin ƙasar na bana.
Cikin tawagar sanatocin da ta ziyarci Fadar Shugaban Ƙasar har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sanata Ningi wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa kuma Shugaban Kwamitin Kidayar Al’umma na Majalisar Dattawa, ya yi murabus daga duk mukaman bayan hukuncin da aka ɗauka a kansa.
An dai dakatar da Sanata Abdul Ningi a ranar Talata, bisa zargin da ya yi na cewa an yi cushe naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin 2024.
Dakatar da Sanatan na zuwa ne bayan da aka yi wani zama da aka yamutsa hazo a zauren majalisar.
Wani mamba a kwamitin Kasafin Kuɗi a Majalisar Dattawa, Jimoh Ibrahim ne ya fara gabatar da ƙudirin dakatar da Sanata Ningi na tsawon wata 12, bisa zarginsa da ba da bayanai ba daidai ba waɗanda suke daidai da aikata babban laifi, da kuma hargitsa zaman lafiya a Majalisar Dokoki da ma ƙasar baki ɗaya.
Wasu ‘yan majalisar kamar Sanata Asuquo Ekpenyong sun goyi bayan ƙudirin Ibrahim ɗin.
Amma Ekpenyong, ɗan majalisa mai wakiltar Kuros Riba ta Kudu da kuma Sanata Abdulfatai Buhari daga Oyo ta Arewa, sun roƙi a rage tsawon dakatarwar zuwa wata shida da uku.
Akpabio, wanda ya bayyana laifukan Ningi a matsayin ‘manya’, ya gudanar da wata ƙuri’a da baki inda mafi yawan ’yan majalisar suka amsa amincewa da dakatar da Ningi na tsawon wata uku.