✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma sun daina zuwa gonakinsu saboda fargaba – Gwamnan Neja

Gwamnan ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen yakar ta'addanci a jihar.

Gwamnan Jihar Neja, Umar Muhammed Bago, ya ce wasu daga cikin manoman Jihar sun daina zuwa gonakinsu don yin noma saboda fargabar za a iya kai musu hari.

Ya kuma koka da munanan ayyukan ‘yan fashin daji da barayin shanu da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da ya ce sun hana ‘yan jihar sakat.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da Kwamandan hukumar tsaron ta Sibil Difens a Jihar, Ahmed Abubakar Audi, ya kai masa ziyara a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar, Babawale Afolabi, ya sanyawa hannu a ranar Laraba.

“Ana kiran jihar Neja jihar samar da abinci, saboda girman filin noma da muke da shi.

“Amma matsalar tsaro da ke kara ta’azzara ta sa mutanenmu a kullum suna kauracewa gonakinsu.”

Gwamnan wanda ya kuma yi Allah wadai da munanan ayyuka da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Jihar ya yi alkawarin ci gaba da yin aiki kan yadda za a samar da ingantaccen tsaro a Jihar.

Da yake jawabi yayin taron, Audi ya yi alkawarin kara habaka dangantakar aiki da hukumar NSCDC da sauran hukumomin tsaro domin kawar da duk wasu miyagun laifuka da suka addabi jihar a baya-bayan nan.

Ya ce rundunar za ta karfafa hadin gwiwarta da sauran jami’an tsaro.