✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar: Mayakan ISWAP sun fara dawowa Arewacin Najeriya

Masana sun ce hakan na dauke da babbar barazana ga yankin

Mayakan ISWAP daga yankin Sahel da Jamhuriyar Nijar suna kwarara zuwa Arewa maso Yammacin Najeriya da kuma Tafkin Chadi bayan juyin mulkin Nijar

Wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa kungiyar ISWAP na kwarara da muggan makamansu daga yankin Sahel ne saboda fargabar shirin dakarun ECOWAS na fada wa Nijar da yaki domin dawo da hambararren Shugaban Kasar, Mohamed Bazoum, kan kujerarsa.

“Manyan mayakan ISWAP sun fara shigowa daga Sahel/Nijar zuwa yankunan Kukawa, Abadam, Gaidam da kuma Guzamala a Najeriya, da kuma Yankin Tafkin Chadi.

“A jihohin Arewa maso Yamma na Katsina, Kaduna, Zamfara da Sakkwato, tuni aka fara fuskantar kwararowar irin wadannan mayakan daga Jamhuriyar Nijar,” in ji majiyar.

Wasu majiyoyi biyu daga cikin sojoji sun ce lamarin ya fara tabarbarewa ne lokacin da aka yi zargin Shugaban mulkin soja na Nijar ya fice daga yarjejeniyar dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF).

“Hakan ya fara kawo babbar barazana ga tsaron yankin Tafkin Chadi.

“Muna ci gaba da sa ido a yankin, amma ina mai tabbatar maka ana samun dimbin ’yan ta’addan ISWAP da ke yin kaura daga yankin Sahel zuwa jihohin yankin Tafkin Chadi. Amma a ’yan kwanakin nan sun fara shiga ma jihohin Katsina da Zamfara da Yobe.

“Manyan mayakan ISWAP da suka hada da Abubakar Modu da Shiek Ba’ana Dujum da Marte Alwady da Mohammed Ibn Abubakar da kuma El-Mansur Dawahli Mouda da ma daruruwan mayakansu, na ta kwararowa.

“Wannan ba karamar barazana ba ce ga yankin.”

To sai dai masu ruwa da tsaki a Jihar Borno na ci gaba da nuna damuwarsu da shirin da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasahen Yammacin Afirka (ECOWAS) ke kokarin yi na daukar matakin soji a kan Nijar.

Mutane da dama dai sun yi amannar cewa daukar matakin zai iya haifar da mummunan sakamako da ilahirin yankin Tafkin na Chadi da ma wasu Jihohin Arewa maso Yamma.

Daga: Hamis Kabir Matazu, Olatunji Omirin (Maiduguri) da Sagir Kano Saleh (Abuja) da Sani Ibrahim Paki