✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A shirye Rasha take ta taimaka wa abokan gabar kasashen Yamma – Putin

A shirye Rasha take ta taimaka wa abokan gabar kasashen Yamma - Putin

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce a shirye kasarsa take ta dada bunkasa alaka da kasashen da za su juya wa kasashen Yamma baya domin su fara hulda da ita.

Ya ce kasarsa, wacce a yanzu haka take fafata yaki da Ukraine da ita kuma ke samun taimakon kasashen Yamma, za ta bayar da tallafin fasaha da na sojoji ga irin wadannan kasashen.

Kamfanin dillancin labaran Rasha, Anadolu, ya rawaito cewa Putin ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabinsa ta bidiyo da aka yada ga dakarun kasarsa da ke kasashen duniya a birnin Moscow.

A cewarsa, “Kofar Rasha a bude take ta dada kulla alakar sojoji da ta fasaha da sauran kasashe da ma kowa da kowa wajen kare martabar kasashensu domin su samu ci gaba.

“Samar da daidaitaccen tsarin tsaro da ba zai fuskanci barazana ba daga waje yana da matukar muhimmanci,” in ji shi.

Kalaman na shugaba Putin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum a Jmhuriyar Nijar, sannan suka nemi tallafin kasar ta Rasha.

Su ma kasashen Mali da Burkina Fasa wadanda su ma suke karkashin mulkin na soja sun nuna bukatarsu ta juya wa Faransa da sauran kasashen Yamma baya, domin su koma wajen Rasha.

Bayan juyin mulkin na Nijar dai, Shugaba Putin ya ziyarci Shugaban mulkin soja na Burkina Faso, Kanal Ibrahim Traore, sannan ya kira takwaransa na Mali, Assimi Goita, ta waya.

Kodayake Putin ya ce ya yi kira da a yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware rikicin siyasar kasar, amma wasu bayanai na nuna cewa yana son yin amfani da yawan juyin mulkin da ake samu a kasashen wajen fadada tasirin kasarsa a yankin.