Birtaniya ta bayyana shirinta na tallafa wa kasar Ukraine da tallafi mafi girma a yaƙin da take yi da ƙasar Rasha.
Firayim Minista Rishi Sunak ya bayar da bayani kan tallafin na fam miliyan 500 (kimanin dalar Amurka miliyan 620m) yayin wata ziyara a Poland.
Ukraine dai ta yi kira da a ƙara ƙaimi taimaka mata a daidai lokacin da dakarun Rasha suka fara kai farmaki a fagen daga tare da ƙara kai hare-hare ta sama.
Birtaniya ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙoƙarin tura wani tallafin kimanin Dala biliyan 60.
Kuɗaɗen za su kai jimillar taimakon sojan Burtaniya da za a bai wa Ukraine zuwa fam biliyan 3 (dala biliyan 3.71) a cikin kasafin kuɗin wannan shekarar, in ji gwamnatin Burtaniya.
Sabon ƙunshin tallafin zai ba da dmar samar da harsasai, matakan tsaro na sama, jirage marasa matuƙa da tallafin injiniyoyi.
Gwamnati ta ce “za a siyo jiragen marasa matuƙa a Burtaniya kuma kuɗaɗen za su taimaka wajen bunƙasa samar da tsaro na cikin gida”.
Abin da Burtaniya ke kira “ƙunshin kayan aiki mafi girma da aka taɓa yi” zai kuma haɗa da jiragen ruwa 60 da sama da makamai masu linzami 1,600 da makami mai linzami da kuma makamin da ake harba shi a iska na dogon zango da madaidaitan makamai masu linzami.
Fiye da motoci 400 da suka haɗa da 162 masu sulke, za a kuma kai su da harsashi miliyan 4 na ƙananan makamai.