✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen Soji Sun Kashe Kwamandojin ISWAP A Borno

Sama da mayaƙan kungiyar ISWAP 30 sun sheka lahira bayan sojojin sama Najeriya sun yi musu ruwan bama-bamai a Borno

Farmakin Rundunar Sojin Saman Najeriya a maboyar ‘yan ta’addar ISWAP ya hallaka sama da kwamandojin ‘yan bindiga 30 a kauyen Kolleram da ke gabar tafkin Chadi, a Jihar Borno.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya sanar cewa daga cikin manyan kwamandojin ’yan ta’addan da aka kashe a harin akwai Ali Dawud da Bakura Fallujah da kuma Malam Ari.

Sanarwar da Gabkwet, ya fitar ranar Talata a Abuja ta ce jiragen yakin Operation Hadarin Kai na Sojin Saman Najeriya sun kai farmakin ne ranar Asabar 13 ga Afrilu.

Ya bayyana cewa, harin ya yi wa ’yan ta’addanci mummunan illa a yankin Arewa maso Gabas, wanda hakan wata garumar nasara ce ga yunkurin dakile ta’addanci a yankin.

“Bugu da kari, harin ya lalata motocin ’yan ta’adda da dama da babura, da kayayyakin amfaninsu, wanda hakan cikas ne ga ayyukan ‘yan ta’addan.

“Bayanan sirrin da aka tattara bayan harin saman sun nuna cewa bama-bamai da aka harba sun lalata wata cibiyar ’yan ta’adda da ke cikin yankin Kolleram, inda suke sarrafa abinci da sauran abubuwa.

“Nasarar wadannan hare-hare ta sama na kara jaddada kudurin Rundunar Sojin Najeriya na kawar da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron ’yan kasa.

“Aikin ya yi matukar nasarar rage karfin kungiyar ISWAP a yankin ta hanyar kawar da manyan ’yan ta’adda da lalata kayayyakin aikinsu.”