✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 10 a Kano

Hukumar ta ce za ta ci gaba da yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Jihar Kano, ta kama wasu mutum 10 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne a watan Yuli.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Sadiq Maigatari ya fitar a Kano, kuma ya raba wa manema labarai ranar Laraba.

Maitagari ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Abubakar Yunusa mai shekara 33 da James Temitope mai shekara 42 da Sani Muhammad mai shekara 23 da Aminu Sani mai shekara 23 da kuma Emeka Williams mai shekara 31.

Sauran sun hada da Inusa Alhassan mai shekara 31 da Muhammad Abubakar mai shekara 35 da Hussaini Hamza mai shekara 45 da Sani Dahiru mai shekara 30 da Muhammad Ibrahim mai shekara 30.

Ya ce an kama su ne a wasu a yankuna daban-daban a jihar.

Maitagari ya kara da cewa an kama wadanda ake zargin dauke da buhun tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,556 da sauran kwayoyi.

A cewarsa, an kuma kama wasu allurai 2,000 na Pentazocine da kuma kwalabe 48 na maganin codeine mai nauyin kilogiram 4.8.

Ya bayyana cewa hukumar ta yi musu cikas wajen raba kayan a jihar tare da yakar masu safarar miyagun kwayoyi.

“Za mu ci gaba da kare al’umma daga illolin shan miyagun kwayoyi,” in ji Maitagari.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga NDLEA a matsayin gudunmawar da za su bayar wajen gina jihar Kano ta hanyar yaki da miyagun kwayoyi.