Daga Itodo Daniel Sule
Majalisar Wakilai ta umarci hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC) ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take.
Wakilin Mazaɓar Dala dake jihar Kano, Ali Sani Madakin Gini (NNPP) ne ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren majalisar.
Madakin Gini ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya sun nunnuka kuɗin makaranta sakamakon hauhawar farashi da ƙarancin kuɗin tafiyarwa da suke samu daga gwamnati.
Usman Kumo, Aliyu Madakin Gini sun zama jagororin Majalisar Wakilai
Majalisar Dokokin Bauchi za ta fara amfani da Hausa a yayin zamanta
Ya ce daga cikin jami’o’in da suka yi wannan ƙarin akwai Jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Jami’ar Najeriya dake Nsukka (UNN), Jami’ar Jos, da Jami’ar Noma ta Michael Okpara.
Ɗan Majalisar ya bayyana damuwar cewa an yi ƙarin kuɗin ne lokacin da al’ummar Najeriya ke fama da tsananin talauci, rashin aikin yi, da hauhawar farashi sanadiyyar janye tallafin man fetur.
Ya ce ƙarin kuɗin jami’o’in zai kawo tarnaƙi ga karatun ɗalibai da dama da ba za su iya biya ba.
Bayan gudanar da muhawara, Majalisar ta amince da wannan ƙudiri kuma ta umarci NUC ta dakatar da ƙarin nan take.
Sannan ta umarci kwamitin Ilimi mai zurfi da zarar an kafa shi, ya lalubo hanyar da za a samawa jami’o’i ƙarin kuɗin shiga ba tare da an ɗora wa ɗalibai da iyayensu nauyin ba.