✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Usman Kumo, Aliyu Madakin Gini sun zama jagororin Majalisar Wakilai

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo (APC-Gombe) da Aliyu Sani Madakin Gini (NNPP-Kano) cikin ƙunshin jagororin majalisar. Honorabul Tajuddeen Abbas ya…

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo (APC-Gombe) da Aliyu Sani Madakin Gini (NNPP-Kano) cikin ƙunshin jagororin majalisar.

Honorabul Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo a matsayin mai tsawatarwa ɓangaren masu rinjaye.

Ya kuma bayyana Aliyu Sani Madakin Gini a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama jagororin Majalisar Dattawa

Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi

Sauran jagororin da shugaban majalisar ya bayyana a ɓangaren masu rinjaye sun haɗa da Julius Ihonvbere a matsayin shugaba, Abdullahi Halims mataimakin shugaba, da Adewumi Onanuga mataimakin mai tsawatarwa.

A ɓangaren marasa rinjaye kuma, Honorabul Abbas ya sanar da Kingsley Chinda a matsayin shugaba, Ali Isa mai tsawatarwa da George Ozodinobi mataimakin mai tsawatarwa.