✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi

Majalisar ta bukaci daidaita al'amura don saukakawa talakawa yanayin da ake ciki.

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta aiwatar da alkawarin da ta dauka na samar da matakan dakile illolin cire tallafin man fetur ga ’yan Najeriya.

Kiran ya biyo bayan amincewa da kudirin da Aliyu Sani Madaki (NNPP, Kano) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya bayyana cewar cire tallafin ya sanya farashin litar man yin tashin gwauron zabo daga N194 zuwa sama da N500, a wasu jihohin ma har sama da haka.

Ya ce, tun a wancan lokacin ’yan Najeriya ke fama da hauhawar farashin litar man fetur da kuma illar da ke tattare da abinci da ayyuka da su ma suka yi tashin gwauron zabon.

Ya ce akwai bukatar a samar da matakan kare hakkin ’yan kasa tare da ba da fifiko wajen samar da kayan agaji domin dakile kalubalen da zai taso game da cire tallafin da kuma tabbatar da tsarin tattalin arziki mai dorewa da hada kan ’yan Najeriya.

Majalisar ta kuma wajabta wa Kwamitinta na Kwadago da ya duba batun tare da bayar da rahoto don ci gaba da aiwatar da aikin.

Shugaba Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Hakan ya sanya tashin farashin man fetur, lamarin da ya tilasta tashin kudin sufurin ababen hawa da wasu kayan masarufi.