✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto manoma 10 da aka sace a Zamfara

'Yan bundigar sun tsere sun bar mutanen da suka sace.

Dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji a Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sun ceto wasu manoma 10 da aka yi garkuwa da su a jihar.

An ruwaito cewa ’yan bindiga sun tsere sun bar wadanda lamarin ya rutsa da su ne a lokacin da suka lura da sojojin na zuwa maboyarsu.

Bincike ya kuma nuna cewa ’yan ta’addan sun yi awon gaba da mutanen ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar 6 ga watan Yuni.

Wadanda aka ceto sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun gudu sun bar su a lokacin da suka samu labarin cewa sojoji na shirin kawo musu hari.

Tuni aka mika manoman da aka ceto zuwa babban asibitin garin Tsafe domin duba su kafin mika su iyalansu.