✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya dakatar da Shugaban EFCC daga mukaminsa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kori Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kori Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar da maraicen Laraba.

Sanarwar ta ce, “Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Abdurasheed Bawa daga shugabancin hukumar EFCC har sai abin da hali ya yi domin a sami damar bincikarsa kan abubuwan da ya yi lokacin da yake ofis.

“Hakan ya biyo bayan wasu zarge-zarge masu nauyin gaske da ake yi masa. Ana umartarsa da ya gaggauta mika ragamar shugabancin hukumar ga Daraktan Gudanarwarta, har zuwa lokacin da za a kammala binciken,” in ji snaarwar.

Matakin dai na zuwa ne kasa da mako daya bayan Shugaban ya kuma dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda shi ma za a bincike shi.

Akwai dai zarge-zarge masu yawan gaske a kan Abdulrasheed Bawa, amma na kwana-kwanan nan shi ne wanda tsohon Gwamnan Jihara Zamfara, Bello Matawalle, wanda ya zarge shi da neman cin hancin Dalar Amurka biliyan biyu, zargin da Bawan ya musanta.