✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje na son kotu ta hana EFCC bincikensa kan bidiyon Dala

Ganduje dai ya sha karyata bidiyon tun a baya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdulahi Umar Ganduje, ya bukaci Babbar Kotun Jihar da ta hana Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC daga ci gaba da bincikensa kan bidiyon Dala.

A shekara ta 2018 ce dai wata jaridar intanet mai suna Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo indas a cikinsu ake zargin Ganduje da karbar cin hanci da Dalar Amurka, daga hannun wasu ’yan kwangila.

To sai dai a kwafin wata kara da Gandujen ya shigar, wacce Aminiya ta yi tozali da ita, ya nemi kotun da ta bayyana cewa bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki, haramun ne EFCC ta binciki lamarin wanda tuni yake gaban Majalisar Dokokin Jihar.

An dai shigar da karar ne ranar 23 ga watan Maris, ’yan kwanaki kafin tsohon Gwamnan ya mika ragamar mulkin jihar.

Kazalika, bincike ya nuna an kai wa EFCC takardun kotun ne ranar 5 ga watan Maris.

Lauyoyin da suka shigar da karar a madadin Babban Lauyan Jihar sun tabbatar mana da cewa har yanzu karar tana gaban kotun, amma sun yi alkawarin bincikawa su yi mana karin bayani kafin zama na gaba.

Masu karar sun kuma bukaci kotun ta bayar da umarnin da zai hana “wadanda ake karar ko jami’anta ko ’yan korarta ko wasu da za ta fake da su ko ta wacce fuska daga ci gaba da gayyata, bincika, yin titsiye ko kuma daukar kowanne irin mataki ta kowacce fuska da ke da alaka da bidiyon Dala a kan Ganduje har sai Majalisa ta kammala nata binciken.”

Idan za a iya tunawa, Ganduje tun a lokacin ya sha karyata sahihancin bidiyoyin, inda ya ce kagaggu ne.

Daga bisani dai Majalisar ta kafa kwamitin a lokacin, kodayake har zuwa karshenta ba ta bayyana wa jama’a sakamakon binciken nata ba.