An gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele kan wasu sabbin tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi kashe naira biliyan 18.96 wajen buga takardun kuɗi na naira miliyan 684.5.
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ce ta gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Maryann Anenih ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ƙasar ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsa.
- Yadda Kasuwar Dare ke neman fin ta rana a Kalaba
- An yi wa malamin makaranta daurin rai da rai kan fyade
A tuhume-tuhume guda huɗu da hukumar EFCC ta gabatar, ta yi zargin cewa Emefiele ya saɓa wa umarnin kotu a lokacin da ya aiwatar da manufar sauya takardun naira a lokacin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A cewar EFCC, tsohon gwamnan na CBN “ya bijire wa umarnin doka da nufin raunata jama’a” ta hanyar amincewa da buga takardun naira ba tare da samun amincewa kai tsaye daga Buhari da hukumar CBN ba.
EFCC ta kuma bayyana cewa ana tuhumar Emefiele ne da amincewa da fitar da Naira biliyan 124.8 daga asusun kuɗaɗen shiga na haɗaka “ta hanyar da majalisar dokokin ƙasar ba ta tsara ba”.