✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Kasuwar Dare ke neman fin ta rana a Kalaba

Duk wani ɗan Arewa da ke buƙatar abincin Arewa, zai samu kowane nau’in abincin Arewa.

An shafe shekaru ana cin Kasuwar Dare a Unguwar Hausawa da ke Kalaba, Fadar Jihar Kuros Riba.

Kasuwar wacce ta fara kamar da wasa, sai ƙara bunƙasa take kuma tana fara ci tun daga kusan Sallar Magariba zuwa ƙarfe 9:00 na dare a kullum.

Aminiya ta ziyarci kasuwar, inda ta tarar da kasuwar na tsaka da ci, mutane suna ta hada-hada kamar yadda aka saba.

Aminiya ta lura mafi rinjaye ana sayar da takalma ne iri daban-daban da suka haɗa da na samari da na ’yan makaranta da sauran takalma.

Shugaban ’Yan Kasuwar, Yusuf Miga, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ni na fara tsugunawa a gefen hanya da ’yar lemata ina sayar da takalma a nan.

“Idan ruwa ya zo sai in kwashe kayan, ko in rufe su da leda in koma gefe in fake, musamman idan kuma ana yin ruwan sama mai yawa kamar yadda aka saba da yake ana ɗaukar watanni masu yawa ana ruwan sama a nan Kalaba.”

Ya ce “Takalma iri daban-daban ake sayarwa a kasuwar ta dare, akwai na yara ’yan makaranta, akwai sau ciki da na buga ƙwallon ƙafa da sauran wasannin motsa jiki da sauran takalman matasa ’yan gayu.”

Bayan masu sayar da takalma, Aminiya ta yi kiciɓis da ɓangaren masu sayar da kifi da masu sayar da lemu da masu sayar da nama da sauransu a kasuwar wadda take ci na kusan awa huɗu a kullum.

Haka kuma kasuwar ta bayar da dama ga duk wani ɗan Arewa da ke buƙatar abincin Arewa, domin a kasuwar akwai kowane nau’in abincin Arewa.

Aminiya ta kuma ci karo da masu sayar da gwanjo da magunguna da kayayyakin amfanin yau da kullum.

Wani mai suna Salisu Baƙo da ke sayar da ruwa ya yi bayani kan irin sauyin da zamani ya kawo da kuma ƙarin farashi kan yadda ake sayar da ruwan, inda ya ce yanzu dole suna ƙara farashin jarkar ruwan saboda yanayin lokacin da ake ciki.