Majalisar Wakilai ta yi watsi da ƙudirin dokar da ke neman mayar da wa’adin shugaban ƙasa da gwamnoni shekara shida.
Majalisar wadda ta dauki matakin ne a ranar Alhamis kan dokar wadda Honorabul Ikenga Imo Ikenga Ogochinyere da wasu takwarorinsa 33 suka gabatar.
Wasu daga cikin tabade-tanaden ƙudirin da aka yi watsi shi sun haɗa da neman a riƙa gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda a Nijeriya.
Bayan Ogochinyere ya gabatar da ƙudurin domin karatu na biyu ne shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya nemi jin ra’ayin mambobi, inda masu adawa da shi suka yi rinjaye.