✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ce kaɗai jam’iyyar adawa mai ƙarfi a Najeriya — Saraki

Saraki ya ce jam'iyyar tana yin shiri cikin tsanaki domin ƙalubalantar APC a 2027.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya.

Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027.

Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin.

Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar.

“PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi.

“Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna samun ci gaba. Mutane suna dawowa cikin jam’iyyar, kuma sabbin mambobi suna shigows. Wannan yana nuna cewa har yanzu jam’iyyarmu tana da ƙarfi.”

Ya ce ana ci gaba da gyara jam’iyyar domin ta zama mai haɗin kai da ƙarfi.

Ya ce tarukan shugabannin jam’iyyar da sauran ayyukan sulhu suna nuna alamun nasara.

“Mun fara shiri tun da wuri, kuma muna da shekara biyu kafin zaɓe. Wannan zai ba mu isasshen lokaci mu shirya,” in ji Saraki.

“Ko da wasu za su bar jam’iyyar, da dama za su shigo cikinta.”

Saraki, ya kuma sabunta rajistarsa a matsayin mamba na PDP, kuma ya ce yana farin ciki da irin goyon bayan da ya gani daga ’ya’yan jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu.

Ya ce wannan yana nuna cewa mutane har yanzu sun yi imani da PDP.

Ya danganta sabon goyon bayan da PDP ke samu da rashin jin daɗin mutane game da yadda ake mulki a matakin tarayya da na jihohi musamman game da rashin tsaro, rashin ayyukan yi, yunwa da kuma rashin shugabanci nagari.

“Mutane sun gaji da halin da ake ciki. Suna son ganin shugabanci na gaskiya ya dawo. Wannan shi ne abin da PDP ke wakilta,” in ji shi.

Saraki, ya tabbatar wa ’ya’yan jam’iyyar da magoya baya a faɗin ƙasa cewa PDP za ta ci gaba da yin sulhu da sake gina jam’iyyar don ta cika burin ‘yan Najeriya.

“Dimokuraɗiyya ba za ta yiwu ba idan babu adawa. Dole ne mu kasance a shirye mu sadaukar da kai da haɗin gwiwa don ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya. Wannan ne abin da PDP ta tsayawa a kai,” in ji shi.