✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta tabbatar da Cardoso a matsayin sabon Gwamnan CBN

Majalisar ta amince da nadin nasa biyo bayan tantance shi a ranar Talata.

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Dokta Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Majalisar ta kuma tabbatar da nadin Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Philip Ikeazor da kuma Dokta Bala M. Bello a matsayin Mataimakan Gwamnan babban bankin.

An tabbatar da su ne biyo bayan tantance su a kwamitin zauren majalisar ya yi.

A ranar 15 ga watan Satumba ce Shugaba Tinubu, ya amince da nadin Cardoso a matsayin sabon Gwamnan na CBN.

Ya kuma amince da nadin mataimakan gwamnan su hudu na tsawon shekaru biyar kowanne a matakin farko, har sai Majalisar ta tabbatar da su.

%d bloggers like this: