✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta sanar da ranar zaben Gwamna a Edo da Ondo

Kwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan jama'a ne ya bayyana hakan

Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da ranakun da za a gudanar da zaben Gwamnoni a Jihohin Edo da Ondo.

Hukumar ta ce za a yi zaben Edo ne ranar 21 ga watan Satumba, yayin da na Ondo za a yi shi ne ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2024.

INEC ta ce sanarwar ta yi daidai da tanadin sashe na 178 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da ya bukaci a yi zabe kafin wa’adin na kai ya ƙare.

Kazalika, sashe na 28(1) na Dokar Zabe ta Kasa ta 2022 ta bukaci hukumar ta sanar da ranar da za a yi zabe cikin kimanin kwana 360 kafin ranar zabe.

A cikin wata sanarwa da Kkwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan jama’a, Sam Olumekun, wa’adin Gwamnan Edo zai kare ranar 11 ga watan Nuwamban 2024, yayin da na Ondo zai kare ranar 23 ga watan Fabrairun 2025.

INEC ta kuma ce nan ba da jimawa ba za ta wallafa cikakkun bayanai kan zabukan a shafukanta na sada zumunta da na intanet.