✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta sahale wa Tinubu ya kashe N500bn don rage radadin cire tallafin mai

Tinubu ya ce za a raba kudaden ne ga talakawan Najeriya

Majalisar Wakilai ta amince wa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kashe Naira biliyan 500 ga ’yan Najeriya domin rage radadin cire tallafin man fetur din da gwamnatinsa ta yi.

An amince da kudurin bukatar ne bayan an yi masa karatu na uku sannan an saurari rahoton kwamitin da majalisar ta dora wa alhaki a kan haka.

Za a debo kudaden ne daga kwarya-kwaryar kasafin kudi na Naira biliyan 819.5 na shekara ta 2022.

Tun da farko dai, dan majalisa Julius Ihonvbere (APC, Edo) ne ya gabatar da kudurin domin a yi masa karatu na biyu, inda Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda (PDP, Ribas), ya goyi bayansa.

Idan za a iya tunawa, a ranar Talata ce Shugaba Tinubu ya aike da bukatar neman amincewar ga zauren majalisar.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas ya karanta a zauren majalisar.

Tinubu ya ce daukar matakin ya zama wajibi domin a ba gwamnati damar samar da abubuwan da za su rage wa jama’a radadin janye tallafin man.

Wasikar ta ce, “Na rubuto ne ina rokon ku yi wa kasafin 2023 kwaskwarima. Hakan ya zama wajibi saboda mu lalubo hanyoyin samar wa da ’yan Najeriya rage radadin cire tallafin man fetur din da muka yi.”

Shugaban ya bukaci ’yan majalisar su ba bukatar tasa kulawa ta gaggawa domin ba gwamnatinsa damar samar wa ’yan Najeriya hanyoyin rage radadin.

Bayan karanta wasikar, Abbas ya ce a ranar Alhamis mai zuwa ce majalisar za ta fara zama domin duba bukatar ta Tinubu.