✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan matan da ba sa zuwa makaranta sun fi masu zuwa yawa a Borno – Zulum

Ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da 'yan mata 500,000 makaranta

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce ’yan matan da ba sa zuwa makaranta a fadin Jihar sun fi wadanda ke zuwa.

Ya ce dalilin haka ne ma ya sa gwamnatinsa ke matukar sha’awar shigar da ’ya’ya matan makarantu domin ceto su daga halin da suke ciki.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta sanya dubban ’yan matan da ba sa zuwa makaranta a ci gaba da shirin karbar ’yan mata 500,000 a makarantun firamare na gwamnati a fadin jihar.

Ya bayyana hakan ne a Maiduguri, babban birnin Jihar, lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, tare da Malala Yousufzai, mai fafutukar ilimin mata kuma jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya.

Malala Yousufzai dai ta zo Najeriya ne domin bikin cika shekaru 10 na jawabinta na farko a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma bikin ranar Malala.

Kowace ranar 12 ga Yuli, Majalisar Dinkin Duniya na bikin ranar Malala don girmama ta, inda ranar ta yi daidai da ranar haihuwarta, a matsayin wata alama ta girmama rayuwarta ta ban mamaki da ta sadaukar wajen fafutukar kwato ’yancin yara da mata.

Da yake halartar bikin karramawar, Gwamna Zulum ya ce ilimin ’ya’ya mata shi ne jigon magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki a tsawon lokaci.

Da take magana tun farko, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed ta ce, “Muna nan (Maiduguri) Mai girma Gwamna, domin a nan ne Malala ta fara kokarinta a Najeriya na neman ilimin ’ya’ya mata, da kare lafiyarsu da iliminsu da kuma yadda za a samu ilimi, ci gaban da za a samu a nan gaba ta yadda su ma za su hada kai da al’ummarsu da jiharsu da kuma Najeriya don zama wani bangare na tattalin arzikinsu”.

Har ila yau, Malala ta bayyana kyakkyawan fata game da makomar ilimin ’ya’ya mata.

Ta ce, “Su (’yan mata) sun jajirce, sadaukarwa da kuma fatan samun makoma mai kyau Ina murnar cika shekaru 10 na jawabina na Majalisar Dinkin Duniya.

Ta kara da cewa, “Tun daga jawabin da na yi na Majalisar Dinkin Duniya, na yi balaguro zuwa kasashe daban-daban na duniya, domin ina son kawo labaran wasu ‘yan mata Jama’a sun ji labarina kuma sun fahimci yadda mace daya ta samu ilimi, don haka muna so mu tunatar da duniya cewa ta yi tunanin sauran miliyoyin ‘yan matan da ba su da damar yin karatu.”

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta kasance a Maiduguri ne tare da Ko’odinetan Majalisar na Najeriya, Matthias Schmale, mahaifin Malala, Ziauddin Yousafzai da wasu jami’an Majalisar Dinkin Duniya.

Uwargidan gwamnan jihar Borno, Dakta Falmata Babagana Umara Zulum, wacce ta tarbi tawagar a filin jirgin sama na Maiduguri, ita ma ta halarci ganawar da Gwamnan.