Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan nazarin rahoton kwamitocin da ke kula da ɓangaren shari’a, ‘yancin ɗan Adam da al’amuran shari’a da miyagun ƙwayoyi da magunguna da ke karkashin Dokar Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) da aka yi wa kwaskwarima a 2024.
- An kama mai maganin gargajiya kan kisan ɗaliba a Edo
- Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da ’yarsa kan N200m
Shugaban Kwamitin, Sanatan Borno ta Arewa Mohammed Monguno na jam’iyyar APC ne ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.
Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na uku, yana da nufin sabunta jerin miyagun ƙwayoyi masu haɗari, da ƙarfafa ayyukan hukumar ta NDLEA, da sake duba hukuncin da za a yanke ga masu fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma ba da damar kafa ɗakunan gwaje-gwaje.
Sashi na 11 na dokar da aka yi a yanzu ya tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi da kotun da ke da hurumi ta same su da laifin. Sai dai ƙudirin dokar na 2024 ya nemi a tsananta hukunci mai tsauri wanda shi ne kisa.
Kodayake rahoton bai bayar da shawarar yanke hukuncin kisa kan laifin ba, inda a yayin nazarin ƙudirin, Sanata Ali Ndume ya yi nuni da cewa a tsananta hukuncin ɗaurin rai da rai zuwa hukuncin kisa.
A yayin da aka yi la’akari da wani sashi na ƙudirin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman na wannan Alhamis ɗin, ya tabbatar da ɗaukar hukuncin kisa ga masu laifin fataucin miyagun ƙwayoyi yayin da mafi rinjayen mambobin majalisar suka kaɗa ƙuri’ar baka ta amincewa da hukuncin.