Mahara sun kashe mutane 33 a wasu kauyuka uku a Karamar Hukuma Bali a Jihar Taraba.
Aminiya ta gano cewa mutanen da aka kashe sun kunshi manoma da makiyaya, akasarinsu Fulani.
A kauyen Garbatau kadai aka kashe mutum 31, da wasu 10 a kauyen Ganfeto, da wasu uku a Hawan Mata, duk cikin kwanaki biyu da suka gabata a karamar hukumar.
Ana zargin wasu bakin Fulani yan sa-kai ne suka kaddamar da hare-haren a kan Fulani makiyaya a yankin.
- Lokutan da Jiragen Sojin Najeriya Suka Jefa Bom Kan Farar Hula Bisa Kuskuren
- Dahiru Bauchi ya nemi Tinubu ya biya jinin Musulmin da jirgin soji ya kashe a Kaduna
Wani mazaunin yankin ya ce yawancin Fulanin yankunan sun kora garken shanunsu zuwa Jihar Adamawa bayan harin.
A sanadiyyar hare-haren, a cewarsa, an sace dabbobi da babuwan wadanda aka kashe.
Kawo yanzu da ba a kai ga gano dalilin harin ba, amma wasu mazauna suna zargin yana da alaka da yaki da ’yan bindiga da mayakan sa-kan suke yi.
Wakilinmu ya nemi bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Taraba SP Usman Abdullahi, amma jami’in bai amsa kiran wayarsa ba.
Amma jami’in ya aiko masa da rubutaccen sako cewa “mun kai ziyarar aiki ne tare da Kwamishina, zan kira daga bisani”
Sai dai har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton ba mu ji daga gare shi ba.