Sashen Hausa na BBC ya bullo da wani sabon shiri mai suna Mahangar Zamani don mata da matasa, wanda za a rika gabatarwa a kafar YouTube.
Shirin Mahangar Zamani, wanda zai rika zuwa da misalin karfe 10 na safiya, bayan kowace Asabar biyu, zai mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi rayuwar mata da matasa, ta hanyar gayyato kwararru da kuma mutanen da ke da alaka kai tsaye da matsalolin da ke ci wa mata da matasa tuwo a kwarya domin jin ta bakinsu.
- Ana yi wa ’yan fim bakin fentin kin zaman aure —Maryam Malika
- Abin da ya hada ni da Adam A. Zango —Ummi Rahab
Da yake magana game da makasudin bullo da shirin wayar da kan, Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko, ya ce, “An shirya shirin ne domin bai wa matasa da mata murya da kuma matsayinsu a cikin al’ummar zamani; Muna son mu kawo wa masu sauraronmu sabuwar mahanga da kuma damar yin muhawara kan muhimman batutuwa.”
Batutuwan da za a rika tattaunawa a Mahangar Zamani sun hada da abubuwan da ke tashe a kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai da sauransu.
A yayin tattaunwar, bakin da aka gayyato zuwa zauren shirin za su fede biri har wutsiya; Akwai kuma bangaren jin ra’ayoyin jama’a kan maudu’in da ake tattaunawa.
A kowane shiri, bayan bakin sun tattauna batun da aka dauko, za su ba da hanyoyin magance matsalolin – wanda shi ne manufar shirin.
Fitacciyar mai gabatar da shriye-shiryen bidiyo, Maidina Maishanu, ita ce za ta jagoranci gabatar da shirin, wanda tsawonsa minti 30 ne kuma zai rika zuwa bayan kowace Asabar biyu.
Kashin farko na shirin Mahangar Zamani zai fito ne a ranar Asabar, 2 ga Oktoba, 2021, kuma zai tattauna ne a kan dambarwar da ke tsakanin dalibai da lakcarori kan zargin yin lalata da dalibai mata kafin su ci jarabawa.