Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da shiga.
Shugaban kungiyar na kasa, Dokta Orji Emeka Innocent, ya shaida wa Aminiya da yammacin Lahadi cewa likitocin za su koma aiki da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Litinin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun raunata wasu a Kaduna
- Hajji: Za mu cika alkawuran da muka yi wa alhazai –NAHCON
Shugaban ya ce, “Za a sake nazarin ci gaban da aka samu a ranar 2 ga watan Yunin 2023 yayin da babban taron kungiya zai yanke shawarar mataki na gaba.”
Kungiyar ta fara yajin aikin ne a ranar Larabar da ta gabata sakamakon abin da ta kira gazawar Gwamnatin Tarayya wajen biyan wasu bukatunta.
Kafin yajin aikin, NARD ta bai wa gwamnati wa’adin mako biyu don biya mata bukatun.
Wasu daga cikin bukatun kungiyar sun hada da karin albashinsu da kasho 200.
Haka kuma, ta bukaci a janye tare da yin watsi da kudirin dokar “marasa hankali” da Ganiyu Johnson ya yi kan zargin tana bautar da matasan likitoci a Najeriya.
NARD ta kuma bukaci a gaggauta biyanta ta asusun horar da ma’aikatan lafiya na 2023 (MRTF) kamar yadda yarjejeniyar da aka cim ma a wani taro da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta kira.
Likitocin sun kuma yi kira da a samar da ababen more rayuwa cikin gaggawa a asibitoci ba tare da bata lokaci ba.
Kungiyar ta kuma bukaci a gaggauta aiwatar da shirin CONMESS, na cikin gida na MRTA, da kuma sake nazartar alawus-alawus daga dukkan gwamnatocin jihohi da kuma cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu inda ake yin kowane irin horo da dai sauransu.