✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya

Likita huɗu ne ke duba mutum dubu 10, adadin da ya yi ƙasa da alkaluman da aka amince da su a matakin duniya.

Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi.

Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata.

Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki da kuma samun cikakken horo, baya ga zurfafa gudanar da bincike a ƙasashen na ƙetare.

Kodayake ya ce, ficewar ƙwararrun likitoci daga ƙananan ƙasashe zuwa ƙasashen da suka ci gaba, ba sabon labari ba ne, amma sai dai adadinsu na ƙara yawaita a shekarun baya-baya nan a cewarsa.

Pate ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda su ma nas-nas da unguwarzoma suka fice daga ƙasar, lamarin da ya ƙara zabtare adadin ma’aikatan lafiyar da ake da su a Najeriya.

A cewar Ministan Lafiyar, kididdiga ta nuna kusan likitoci huɗu ne ke duba mutum dubu 10 a ƙasar, yana mai ƙiyasta sama da Dala dubu 21 a matsayin kuɗin da ake kashe wa kowanne likita guda wajen horas da shi.

“A Najeriya kaɗai, sama da likitoci dubu 16 aka ƙiyasta sun fice daga ƙasar a cikin shekaru biyar zuwa bakwai. Nas-nas da unguwarzoma su ma sun yi ƙaranci.

“Yanzu likita kusan huɗu ne ke duba mutum dubu 10, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da alkaluman da aka amince da su a matakin duniya.”