Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana shirinta na raba kayan abinci da ta kama ga ’yan kasar domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu.
Hukumar ta ce za a yi rabo kayan abincin ne bayan an tantance su an tabbatar da cewa ba su da hadari ga lafiyar dan Adam.
Dubban ’yan Najeriya dai sun gudanar da zanga-zanga a kan tituna kan halin kunci da tsadar kayan masarufi a kasar.
A kan haka ne ranar Talata shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana shirinsu ba raba kayan abincin da aka kama ga ’yan Najeriya.
- Mai Kula da Dakin Kabarin Manzon Allah ya rasu
- Ya kamata Hukumar Kwastam ta sakar wa ’yan kasuwa mara — Sarkin Kano
Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya sanar cewa daukar matakin ya dace da aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na watsa kasa a abinci.
A cewarsa, matakin na gaggawa ne kuma daukar sa na da muhimmanci wajen samun wadatar abinci a Najeriya da kuma dakile illar karancinsa ga ’yan kasa.
“Za a sanar da hanyoyin da za a bi wajen rabon kayan ta ofishin hukumar a duk fadin Najeriya, domin tabbatar da adalci da kuma yin koma a don tabbatar da cewa amfanin ya isa ga wadanda suka fi bukata,” in ji shi.