✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi

Mazauna yankin na ci gaba da damuwa kan yiwuwar sake kai musu hari.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai har iyakar Bachaka da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin garin.

Harin ya faru ne kwana guda bayan da dakarun tsaro suka kashe wasu dakarun Lakurawa a yankin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ba a tantance sunayen jami’an Kwastam da aka kashe ba.

“Eh, an kai hari, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin Bachaka,” in ji kakakin rundunar, Nafiu Abubakar.

Bayan harin, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani Bello, ya ziyarci wajen tare da tabbatar wa jama’a cewa hukumomin tsaro na aiki domin kama waɗanda suka kai harin.

“Waɗannan hare-hare na nuni da cewa miyagun suna raguwa saboda yawan farmakin da muke kai musu.

“Za mu ci gaba da yaƙar su har sai mun kawar da su gaba ɗaya,” in ji CP Bello.

Har yanzu, jama’a na cikin fargaba game da tsaro a yankunan kan iyaka, yayin da suke nuna damuwa kan yiwuwar sake kai musu hare-hare.