Yayin da al’ummar Musulmi ke ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadana, a hannu guda kuma Najeriya na ci gaba da fama da matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
A yanzu dai, farashin kayan ya tashi da kashi 15.70 a kasar da galibin jama’arta ke rayuwa hannu baka hannu kwarya kuma suke cikin mawuyaciyar hali, kamar yadda wakilanmu suka gano.
- 2023: A ba Osinbajo dama ya dora daga inda Buhari ya tsaya – Matasan Arewa
- Tsananin kaunar Tinubu ta sa matashi yin tattaki daga Gombe zuwa Legas
Da daman masu karamin karfi a kasar na ikirarin cewa abubuwa ba su taba lalacewa su zama da wahala kamar haka ba.
Wasu da wakilanmu a Kano da Kaduna suka zanta da su, sun bayyana yadda rayuwar yau ke gara su da kuma irin gwagwarmayar da suke sha wajen sauke faralin azumin Ramadan da halin tsadar rayuwar da ake fuskanta a kasar.
Akwai karancin shirye-shiryen tallafi
An gano cewa babu wasu shirye-shiryen ba da tallafi ga talakawa daga bangaren Jihohi da attajirai da kungiyoyin addini don taimakawa wajen ciyar da marasa galihun da matsalolin rashin tsaro da rashin aiki da talauci suka addabe su a wannan lokaci, idan ma akwai shirye-shiryen, to ba su wadata ba.
Muhammad Sani, wani mazaunin unguwar Dorayi ne a birnin Kano, ya shaida da wakilinmu cewa tun ma kafin zuwan azumin da wahalar gaske shi da iyalinsa suke ci abinci sau biyu a yini.
Magidancin mai ’ya’ya shida ya yi korafin cewa, “Tsadar farashin kayayyaki da yanayin tattalin arzikin kasa sun canja komai. Ba ni ne abin damuwa ba amma iyalina, musamman kananan yaranmu.
“A gaskiya rayuwa ta yi tsada matuka a ’yan kwanakin nan, kuma babu inda za mu je mu roka. Sai dai mu roki Allah Ya kawo mana saukin al’amari.”
Daga nan, ya yi kira ga masu hannu da shuni su fito su taimaka wa talakawa, musamman ma a watan na Ramadan.
‘Kwana uku ba a dora tukunya a gidana ba da azumi’
Shi kuwa Jibrin Musa da ke zaune a yankin Sagagi a Kano, wanda kuma aka shafe kwanaki uku a jere ko tukunya ba a dora a gidansa ba balle a yi batun girki a cikin wannan wata na azumi, cewa ya yi ya yanke shawarar ya rika ziyartar masallatai don neman taimakon abin da za su ci da iyalansa.
“Ina da mata daya da ’ya’ya shida. Sakamakon matsin tattalin arzikin da muke fuskanta mun cinye jarina tun kafin ma a shiga Ramadan, yanzu na rasa sana’ata,” inji Musa cikin yanayi na kuka.
Daga nan, Musa ya yi roki jama’a da cewa, “ina bukatar a taimaka mini da sana’ar da zan rika yi don samun abin da zan ciyar da iyalina.”
A nata bangaren, Larai Mu’azu, wata gyatuma ce mai ’ya’ya bakwai wadda kan fita bara a titunan Kano kafin samun abin da za su ci, ta ce “Kafin zuwan Ramadan, ba mu iya cin abinci sau uku a yini. Sau biyu mukan ci abinci a ranar da harka ta yi kyau, wasu lokutan kuma sau guda tak.”
Larai ta ce shekara daya kenan da rasuwar maigidanta, kuma ya rasu ya bar mata yara bakwai ba tare da samun tallafi daga wajen wani ba.
Ta ce “Duba da halin tsadar rayuwa da ake ciki, na yi yunkurin sau da dama don samar wa kaina da ’ya’yana aiki amma hakan ya ci tura. Wannan ya sa ni da su muka soma bara tun da ba mu da jarin da za mu kama sana’a.”
Gyatumar ta ce yanayi ne ya tilasta mata shiga harkar bara, tare da cewa “babu wani tallafi da muke samu daga ’yan’uwana ko dangin mijina don samun abin da za mu ci kasancewar duka dangin talakawa ne.”
Ta kara da cewa ’ya’yan biyu da suka girma, su kadai ba za su iya ciyar da mu da dan abin da suke samu ba idan sun yi kwadago a kasuwa.
Ta ci gaba da cewa, takan bi wasu gidajen masu hali ne inda a kan raba wa marasa galihu abinci kafin su samu abincin da suke buda-baki da shi.
Da yake bayani a kan halin rayuwarsa, Alhaji Sa’adu Yusuf, wanda dan kasuwa ne mai sayar da abaya a Zoo Road a Kano, ya ce, cinikin da yakan yi a yini ba ya dauke masa hidimar gidansa a wannan watan.
Sai dai kuma, sabanin halin da wasu ke fuskanta gane da ’ya’yansu, Yusuf ya ce shi dai ya taki sa’a domin kuwa, nasa ’ya’yan kan tallafa masa gwargwadon hali idan sun fita sun roro.
‘Tun safe cinikin N2,000 kawai na yi’
Ta bangaren Lawan Maicarbi wanda ke sana’ar sayar da carbi a Kano don kula da iyalinsa, lamarin ba a cewa komai, sai addu’a.
Ya ce “Akalla dai yin wannan sana’ar (sayar da carbi) ya fi zaman kashe wando, yana mai cewa a baya sana’ar na garawa matuka idan aka shiga watan Ramadan, amma a yanzu abubuwa sun sauya.
“Tun safe zuwa kusan karfe 5:00 na yamma, ban yi cinikin N2,000 ba. Dan cinikin da na samu shi mukan lallaba mu yi amfani da shi. Wasu ranakun ma ba na samun abin da zan ciyar da iyalina,” inji shi.
Shi kuwa Muhammad Abdu, wani mai fama da nakasa sannan yana da mata daya da ’ya’ya hudu.
Ya ce baki dayansu sun dogara ne ga bara don samun abinci kasantuwar ba su da sana’a ko wata tsayayyar hanya ta samun abin masarufi.
Ya ce, “Ba sona ba ne, na tsani bara amma yanayi ne ya tilasta min saboda abin da zan iya yi ke nan kawai. Ina fama da nakasa, na rasa hannuwana duka biyu sannan ba ni da wata madogara.
Ya kara da cewa, “Nakan hanzarta in koma gida da zarar na samu abin da za mu ci da iyalina, don kuwa ba ni da wani zabi da ya wuce wannan.”
Ko a sauran jihohi haka lamarin yake, don kuwa ba ta sauya zani a Jihohi irin su Kaduna ba.
A iya cewa ma matslar ta fi kamari a Kaduna ganin yadda da yawan jama’a haka suke tashi da azumi ba tare da yin sahur ba sannan babu tabbacin samun abun buda-baki yayin shan ruwa.
Wani mazaunin yankin Rigasa cikin Karamar Hukumar Igabi a Jihar, mai suna Malam Mohammed Yusuf, ya ce da kyar ya iya samun wake gwangwani biyun da ya kai wa iyalinsa aka yi buda-baki da shi a ranar Talata.
A cewarsa, “A da karantarwa nake yi amma sai aka kore ni daga aiki sakamakon na kasa zuwa zurfafa karatuna. Bayan rasa aiki da na yi, sai na kama harkar sana’o’i daban-daban, da yake ba ni da isasshen jari hakan ya sa na kwashe dan abin da na kalata na yi amfani da shi wajen kula da hidimar iyali.
“A wannan lokaci na azumi kuwa, da kyar nake samun abin da za mu yi sahur da shi, amma da taimakon makwabtanmu muna dan samun abin kaiwa bakin salati lokacin buda-baki.”
Ya kara da cewa, ala tilas ya bari ’ya’yansa suna tafiya aikatau don su samu abin da za su kula da kansu.
‘Azumin bana ya zo a mawuyacin hali’
Har wa yau, wata mazauniyar Kaduna mai suna Hauwa Ibrahim, ta ce azumin bana ya zo a lokacin da jama’a ke cikin mawuyacin hali.
Ta ce kafin zuwan Ramadan, gidaje da dama fama suke da abin da za su ci, gidanta ma na daga cikinsu.
“Ni bazawara ce, mijina ya rasu shekaru biyu da suka gabata, sannan muna da ’ya’ya biyar, tun bayan rasuwar dawainiyar kula da gida ta dawo kaina.
“Ban yi karatu ba sai dai nakan taba ’yar sana’ar da ba ta taka kara ta karya ba, don haka da zuwan azumin nan abun ba a cewa komai.
“Ba don agajin abincin da wata kungiyar mata musulmi ta ba mu ba a unguwarmu Tudun Wada ba, da tuni yunwa ta kai mu ta baro. Hankalina ba a kwance yake ba don kuwa ragowar abincin da aka raba mana ke nan zan girka, daga nan kuma ban san abin da zai biyo baya ba.”
Daga nan, Hauwa ta yi kira ga Musulmi masu hali da su shigo su taimaka wa mutane ire-irenta, musamman ma a wannan wata na Ramadan.
Su kuwa mutane ire-iren Bashir, Yamadawa, Abdu, Maicarbi, Hajiya Larai, Musa da kuma Sani, fata za su kan cewa Allah ya sa shirin ciyar wanda zai lakume miliyan N550 da Gwamnatin Kano ta sanar za ta yi, ya taimaka musu wajen samun sassaucin nauyin da ke kansu, yayin da Amina, Hauwa da kuma Yusuf za su ci gaba da addu’ar Allah Ya bai wa Gwamnatin Jihar Kaduna ikon bin sawun ta Kano wajen samar da shirin da zai tallafa wa marasa galihu, da kuma fatan daidaikun mutane masu hannu da shuni da kungiyoyi za su ci gaba da fadada taimakonsu don amfanin mutane irinsu.
Daga Aminu Naganye da Sadiq Adamu, Kano, Maryam Ahmadu-Suka, Kaduna da Bashir Isah