Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya.
- Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal
- Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
Bankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito.
Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba da tafiyar hawainiya.
Bankin Duniyar ya ce har yanzu mahukuntan Nijeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawan ƙasar ba.
A cewarsa, abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.
Bankin ya ce duk da ci gaban da Nijeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawan ƙasar ta yammacin Afirka.
Rahoton ya jaddada cewa har yanzu yankin ƙasashen Sahel ne ke kan gaba a talauci a duniya gaba ɗaya, yayin da yankin ke da kaso 80 adadin mutane miliyan 695 na mutanen da ke fama da baƙin talauci.