✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙarin ’yan Najeriya za su shiga talauci nan da 2027 — Bankin Duniya

A cewar Bankin Duniya, Najeriya, tare da wasu ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni a yankin kudu da Sahara, za su fuskanci ƙaruwar talauci

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027.

Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.C., a ƙasar Amurka.

Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba.

A cewar Bankin Duniya, Najeriya, tare da wasu ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni a yankin kudu da Sahara, za su fuskanci ƙaruwar talauci —saɓanin ƙasashen marasa arzikin albarkatu, waɗanda ake tsammanin za su samu raguwar talauci cikin sauri.

Rahoton ya bayyana cewa, “Ana hasashen talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari tsakanin 2022 zuwa 2027a ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni—ciki har da manyan masu tattalin arziƙo kamar Najeriya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.”

A halin da ake ciki, Sanatan da ke wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya yi kira ga ƙasashen a Afirka, Bankin Duniya, da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da su ba da fifiko ga amfani da bayanai don ci gaban Afirka.

Da yake magana a yayin taron bazara na IMF/Bankin Duniya a Washington, D.C., Amurka, Sanata Jimoh Ibrahim ya jaddada muhimmancin bayanai a ci gaban tattalin arziki da siyasa.

Ya ce, “Idan babu bayanai ba, babu wanda zai iya rage aikata laifuka yadda ya kamata ko kuma gudanar da gwamnatin da ke da nufin cimma nasarar rage talauci.”

Ya ƙara da cewa, “Bayanai kan yawan jama’a da cikakkun bayanai na mutane sun nuna cewa ya kamata ’yan ƙasa su mallaki fasfo na tantancewa domin tattara muhimman bayanai game da su wane ne su da kuma abin da suke yi.”

Sanatan ya yi gargadi ga IMF game da yin hasashe ba tare da ingantattun bayanai ba, yana mai cewa irin waɗannan hanyoyin ba su da inganci.